Da yammacin ranar Litinin 03, ga watan Rabi'ul Thani, 1447, daidai da 24, ga watan Nuwamba, 2025, 'yan uwa musulmi na da'irar Katsina, suka gudanar da zaman juyayin shahadar Sayyida Fatima (S.A) a muhallin Markaz dake Kofar Marusa.
Sheikh Yakub Yahya Katsina ne ya jagoranci zaman juyayin. A cikin jawabin su Malam, sun taɓo ƙadiyoyi daban-daban waɗanda suka shafi tarihin rayuwar ta, tun daga wafatin mahaifinta Manzon Allah (S), da kuma yadda ya kasance a lokacin da aka tilasta wa mijinta Imam Ali (AS) yi ma Khalifa na farko mubaya'a, da kuma sauran jarabawar da ta fuskanta waɗanda suka yi silar shahadar ta.
Your Comment